Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yanzu haka yana ziyarar aiki a kasar Amurka, bisa gayyatar da shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya yi masa. Wannan ziyara ta shugaban kasar Sin ta zo a lokacin da Sinawa suke murnar bikin gargajiya na Zhong Qiu, wanda ke nuna tsakiyar kaka. A ranar da muke ciki, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun yi ganawa a Washington D.C, gami da halartar bikin liyafa tare.

Lamarin da ya nuna cikakken sahihanci da aminci da ake samu wajen karfafa zumunta da hulda ta hadin kai tsakanin kasashen biyu. Sai dai mene ne tasirin haduwar shugabannin Sin da Amurka ga kasashen Afirka? Dangane da wannan tambaya, Sizo Nkala, masanin ilimin al’amuran duniya, dan kasar Afirka ta Kudu, ya ce yadda shugabannin biyu suka gudanar da cudanya kai tsaye zai samar da damar karfafa fahimtar juna da kyautata hulda tsakanin manyan kasashen biyu.

Abun da ke da matukar muhimmanci ga yunkurin raya tattalin arziki da tabbatar da kwanciyar hankali a duniya. Kana a nasa bangare, Onyango K’Onyango, wani shahararren dan jarida na kasar Kenya, ya ce huldar dake tsakanin Sin da Amurka tana haifar da tasiri kan yanayin tattalin arzikin duniya. Idan kasashen biyu sun iya magance rikici da ci gaba da cudanya da juna, to, dimbin kasashe masu tasowa za su sami damar hadin gwiwa da karin abokan hulda.

Da raya tattalin arzikinsu yadda suke bukata. Sakamakon da aka samu wajen ganawar da shugabannin Sin da Amurka suka yi a wannan karo ma ya nuna cewa, hasashen da masu sharhi na kasashen Afirka suka yi ya yi daidai. Saboda a lokacin da shugabannin biyu ke zantawa da juna, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, kasashen Sin da Amurka za su iya tabbatar da moriyar juna, da daidaita sabanin ra’ayi.

Da karfafa amincewa da juna, da tushen zaman lafiya, a kokarin samar da wata hulda mai kyau tsakanin kasashen biyu, wadda za ta amfani jama’ar kasashen da al’ummun duniya. Kana a nasa bangare, shugaba Trump na kasar Amurka ya ce, tabbas ne za a iya kyautata huldar dake tsakanin kasarsa da kasar ta Sin, bisa jagoranci da shi da shugaba Xi suke yi.

Ban da ganawar da sugabannin biyu suka yi, a kwanan nan, tawagogin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen biyu sun gudanar da zagaye na takwas na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a Amurka. Bangarorin biyu sun yi shawarwari na gaskiya masu zurfi kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya da suka shafe su.

Kamar aiwatar da yarjejeniyar matsayar da aka cimma a tattaunawar tattalin arziki da cinikayya, da aiwatar da tsare-tsaren rage haraji daidai-wa-daida, da kuma kafa majalisun cinikayya da zuba jari, kana sun cimma wasu matsaya da dama. Kazalika, bangarorin biyu sun kuma tattauna a karon farko game da fasahar kirkirarriyar basira ta AI a karkashin tsarin tattaunawar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka.

Key points

  • - Haduwar shugabannin Sin da Amurka ta samar da tabbaci ga al’amuran duniya. - Cudanya da mu’ammalar kasashen 2 sun nuna wani yanayi mai gamsarwa. - Huldar dake tsakanin Sin da Amurka tana haifar da tasiri kan yanayin tattalin arzikin duniya.

Share this story

Written by

SaharaWire Newsroom
SaharaWire

Reporting for SaharaWire from the Nairobi bureau.