Adeyemi Adekunle ya ruwaito cewa wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo inda yayi da'awar cewa Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar III, bai taba magana ba, ko yayi kira da a hada kai a yaki masu fashin daji da 'yanta'adda ba, sai a baya-bayan nan. Bidiyon ya samu martani kala-kala wanda suka rika nuna gazawar ta Sultan na yin magana kan batu na yaki da masu fashin daji da ta'addanci.
Wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 109,000 da masu tsokaci 369 da wadanda suka sake yadawa su 440 da masu nuna sha'awa 1,900. Wani mai amfani da shafin mai suna Chinedu Cornard, ya rubuta cewa, "Saboda suna cikin masu laifi a Amurka, shine yanzu suke magana mai kyau, nan ba da dadewa ba za su zama tarihi, ciki har da wadanda suka rubuta abubuwa a shafukansu marasa dadi kan Amurka daga bisani suka koma suka goge… "
DUBAWA ta gudanar da bincike kan abubuwan da suka shafi wannan da'awa sai ta gano wasu labarai masu alaka. A rahoton kafar yada labaran Channel Television na ranar 10 ga Afrilu,2019 bayan da aka rika samun karuwar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya Sarkin Musulmi yayi alkawari na ba da tallafi a kokari na jami'an 'yansanda da sauran jami'an tsaro don kawo karshen masu fashin daji da sauran ayyuka na miyagun laifuka a Arewacin Najeriya.
Ita ma kafar yada labaran The Cable ta ba da rahoto a ranar 30 ga watan Mayu,2020 bayan hari da aka kai a Sokoto, wanda yayi sanadin rayukan mutane 70 mai sarautar ba kawai yace a "kamo masu wannan ta'addanci ba'' yace matsalar tsaro ta tabarbare a wannan yanki. A ranar 31 ga Mayu,2020 kafar yada labaran Channels TV ta ba da rahoto cewa Sarkin Muslmi yayi kira da a kara yawan kudade da ake kashewa harkokin soja ta yadda za su iya kawo karshen masu fashin daji da sauran miyagun laifuka.
Mai magana da yawun Sultan Mallam Aminu Haliru, ya tabbatar da abin da DUBAWA ta gano inda ya fada mata cewa Jawabin na ranar 9 ga Yuli, 2026 ba shine karon farko ba da Sarkin Musulmi yayi kira da a samar da hadin kai, a kokari na kawo karshen 'yanfashin daji da 'yanta'adda; a lokuta da dama ya sha kira na a duba matsalar tsaro a Najeriya."
A yayin wani taro da Sultan ya halarta a ranar 4 ga Disamba,2025 da kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin ofishin mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da Cibiyar Kukah mai taken "Hada kan kafatanin al'umma," Sultan ya bukaci 'yan Najeriya su hada kai don tunkarar matsalar masu fashin daji bai daya. Da'awar cewa Sarkin Musulmi da ke Sokoto bai taba sukar 'yan fashin daji ba karya ce.
Key points
- Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar III ya sha yin kira na a hada kai a yaki masu fashin daji da 'yanta'adda a Najeriya.