Gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya yi da'awar cewa wani rahoton da UNICEF ta fitar na hasashen wai a shekara ta 2027 ba za'a sami dalibi namiji ko daya ba a aji data na makarantar sakandaren da ke kananan hukumomin Shiroro da Munya a jihar. Bago ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke wata hira a tashar gidan talibijin na Channels a shirin siyasar da sukan yi ranar lahadi mai suna Sunday Politics.
Wannan hirar ta zo ne a daidai lokacin da ake nuna damwa dangane da mutuwar yara 37n da ake zarginsu da hakar ma'adinai ta haramtaciyyar hanya, a hannun jami'an NSCDC na jihar Nejar. An kama yaran da ake zargin ne bayan da aka kai wata samame na neman masu hakar ma'adinan ta bayan fage a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto a ranakun 15 da 16 na watan Satumban shekarar 2026.
A cewar tashar talibijin na Channels Television, yara matasa 67 aka kama inda daga baya 37 daga cikinsu suka rasa rayukansu. Har yanzu ana gudanar da binciken gano abubuwan da suka yi sanadin mutuwarsu. Da ya ke bayani kan tasirin da hakar ma'adinan ke yi kan al'ummomin jihar, Bago ya ce : "Mun san cewa hakar zinari yanzu ya zama ruwan dare.
Rahoton UNICEF kan kananan hukumomin Shiroro da Munya ya ce a shekara ta 2027 ba za'a sami namiji ko daya ba a ajin farko na makarantun sakandaren da ke yankin. Kun gane? Saboda dukansu sun daina zuwa azuzuwa yanku sun koma hakar ma'adinan karkashin kasa. Kuma wannan babbar matsala ce a gare mu."
Dan haka ne DUBAWA ta yanke hukuncin gudanar da bincike kan wannan lamarin domin ya na da mahimmanci ga al'umma musamman ganin yadda ake la'akari da tshar a matsayin daya daga cikin tashoshin da ke da nagarta wajen watsa labarai. Tantancewa Ganin yadda a kai tsaye gwamnan ya ambato UNICEF, DUBAWA ta fara ta yuntubar ofishin UNICEF a Najeriya dan jin ko ta gudanar da bincike kan tasirin hakar ma'adinan a kan daliban sakandaren da ke zuwa makaranta a karamar hukumar Shiroro da wadanda ke kusa da ita a jihar Neja.
Haka nan kuma mun tambayi kungiyar ko za ta iya nuna mana rahoton ta kuma fayyace mana inda ya yi wannan hasashen na rashin dalibai maza a azuzuwan farko na makarantun sakandare sakamakon hakar ma'adinai. Da ta ke mayar da martani ta bakin wakilinsu na musamman kan sadarwa Samuel Kaalu, UNICEF Najeriya ta ce ba ta taba gudanar da bincike irin wannan ba.
"UNICEF ba ta taba gudanar da bincike ko ma bayar da izinin gudanar da bincike kan tasirin hakar ma'adinan kan yanayin zuwa makarantar yaran da ke zuwa hako ma'adinan a karamar hukumar Shiroro da wasu kananan hukumomin da ke jihar NEja ba," Kaalu ya bayyana cikin wani sakon imel din da ya turawa Ko da shi ke ya bayyana cewa UNICEF ta tallafawa wani binciken da aka yi wa taken "Tasirin Rashin Tsaro kan Samar da Ilimi a jihohin Katsina, Zamfara da Neja."
Key points
- Da'awar gwamna Bago na cewa UNICEF ta ce ba za'a sami yara maza a azuzuwan farko na makarantun sakandaren da ke wasu yankunan jiharsa a shekara ta 2027 ba gaskiya ba ne.